Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Kashe Mutane Da Dama A Wasu Asibitoci A Wani Hari Kan Gaza - Likitocin Falasdinu


Israel-Palestinians
Israel-Palestinians

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta ce dakarun Isra'ila sun yi wa wasu asibitoci biyu kawanya a ranar Lahadin da ta gabata, inda suka yi ta luguden wuta kan jami'an kiwon lafiya, daga bisani Isra'ila ta ce ta kama 'yan ta'adda 480 yayin da aka ci gaba da gumurzu a babban asibitin Al Shifa na Gaza

WASHINGTON, D. C. - Isra'ila ta ce asibitocin yankin Falasdinu, inda aka kwashe sama da watanni biyar ana yaki, mayakan Hamas ne ke amfani da su a matsayin sansani. Ya kuma fitar da bidiyo da hotuna masu goyan bayan da'awar.

Saidai ma’aikatan lafiyar Hamas sun musanta zargin.

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce daya daga cikin ma'aikatanta ya mutu a lokacin da tankokin Isra'ila suka koma baya ba zato ba tsammani zuwa yankunan da ke kusa da asibitocin Al-Amal da Nasser a birnin Khan Younis da ke kudancin kasar, yayin da ake ta luguden wuta da harbin bindiga.

Sojojin Isra'ila sun fara ayyukan binciken su kusa da Al-Amal, in ji rundunar sojin, biyo bayan "sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa 'yan ta'adda na amfani da kayayyakin more rayuwa na farar hula wajen ayyukan ta'addanci a yankin na Al-Amal."

A cikin wata sanarwa da kungiyar agaji ta Red Crescent ta fitar ta ce, sojojin Isra'ila masu sulke sun rufe asibitin Al-Amal tare da katse duk wasu ayyuka a kusa da shi.

"Dukkan kungiyoyin mu na cikin hadari sosai a halin yanzu kuma ba su da hanyoyin yin ayyuka gaba daya," in ji ta.

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta ce, a yanzu sojojin Isra'ila na bukatar a kwashe ma'aikata da majinyata da marasa matsuguni daga harabar Al Amal, suna kuma ta harba bama-bamai a yankin domin fatattakar mutanen da ke cikinta.

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta ce an kashe wani Bafalasdine da ke gudun hijira a cikin harabar asibitin bayan da harbi daga ‘yan Isra'ila ta same shi a kai.

Ma'aikatar lafiya a Gaza ta Hamas ta ce sojojin kasar Isra'ila sun tsare marasa lafiya da dama da ma'aikatan lafiya a Al Shifa da ke birnin Gaza a yankin arewacin kasar da ke karkashin ikon Isra'ila na tsawon mako guda.

Red Crescent
Red Crescent

Ofishin yada labarai na gwamnatin Hamas ya ce haka kuma sojojin Isra'ila sun kashe likitocin Falasdinawa biyar a farmakin da suka kwashe kwanaki bakwai suna yi kan Al Shifa.

Sojojin Isra'ila ba su amsa nan take ba kan bukatar jin ta bakinsu kan wannan rahoto. Tun da farko an ce ta kashe 'yan bindiga sama da 170 a harin, wanda ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce ya kuma yi sanadiyar mutuwar marasa lafiya biyar.

Al Shifa yana daya daga cikin 'yan tsirarun cibiyoyin kiwon lafiya da ma ke aiki a wani bangare a arewacin Gaza, kuma kamar sauran shi ma ya kasance matsuguni ne wa wasu fararen hula kusan miliyan 2, sama da kashi 80% na al'ummar Gaza sakamakon yakin.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG