Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Ce A Gudanar Da Bincike Kan Kaburburan Da Aka Gano A Asibitocin Gaza Da Isra'ila Ta Kai Wa Mamaya


Asibitin Gaza
Asibitin Gaza

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira a ranar Talata cewa a yi "bincike dalla dalla, na gaskiya kuma tabbatacce" na wasu manyan kaburbura da aka gano a wasu manyan asibitoci biyu a Gaza da ke fama da yaki da sojojin Isra'ila suka kai wa hari.

WASHINGTON, D. C. - Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya gaya ma manema labarai cewa dole ne ‘yan jarida su samu damar shiga wuraren su kuma samu damar yin aiki cikin aminci a Gaza domin bayar da rahotanni kan gaskiyar lamarin.

Da sanyin safiyar Talata, babban jami'in kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya ce "ya firgita" da lalacewar cibiyar kula da lafiya ta Shifa da ke birnin Gaza da kuma asibitin Nasser da ke birnin Khan Younis wanda ke kudu, da kuma rahoton gano kaburbura a ciki da wajen wuraren bayan Isra'ilawa sun bar wurin.

Ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa na gaskiya kan mace-macen, yana mai cewa "idan aka yi la'akari da yanayin rashin hukunci, wannan ya kamata ya hada da masu binciken kasa da kasa."

Volker Türk
Volker Türk

"Asibitoci na da ikon samun kariya ta musamman a karkashin dokar jinkai ta kasa da kasa," in ji Türk. "Kuma da kashe fararen hula da gangan, fursunoni da sauran wadanda suke 'hors de combat' wato marasa iya yin yaki, laifi ne na yaki."

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Vedant Patel a ranar Talata ya kira rahotannin na samun kaburbura a asibitocin "abin damuwa" kuma ya ce jami'an Amurka sun nemi gwamnatin Isra'ila ta ba da bayanai.

Rundunar sojin Isra'ila dai ta ce dakarunta sun tono gawarwakin da Falasdinawa suka binne tun da farko a wani bangare na neman ragowar mutanensu da Hamas ta yi garkuwa da su a harin da suka kai ranar 7 ga watan Oktoba da ya haddasa yakin. Sojojin sun ce an duba gawarwakin cikin mutunci kuma an mayar da wadanda ba na Isra'ila ba da aka yi garkuwa da su zuwa inda suke.

Vedant Patel
Vedant Patel

Rundunar sojin Isra'ila ta kuma ce ta kashe ko kuma tsare daruruwan 'yan ta'addar da suka samu mafaka a cikin harabar asibitocin biyu, ikirarin da ba a iya tantancewa kansa ba.

Rundunar tsaron farar hula ta Falasdinu a zirin Gaza ta fada jiya Litinin cewa ta gano gawarwaki 283 a wata makabartar wuccin gadi a cikin babban asibitin Khan Younis da aka gina a lokacin da sojojin Isra'ila suka kwace ginin a watan jiya. Kungiyar ta ce a lokacin mutane ba su samu damar binne mamatan a makabarta ba dalili kenan aka tona kaburbura a harabar asibitin.

Hukumar kare hakkin bil adama ta Civil Defence ta ce wasu gawarwakin na mutanen da aka kashe a harin da aka kai wa asibitin ne. Wasu kuma sun mutu a lokacin da sojojin Isra'ila suka kai farmaki kan asibitin.

Jami'an kiwon lafiya na Falasdinu sun ce hare-haren da aka kai kan asibitocin ya lalata bangaren kiwon lafiya na Gaza yayin da take kokarin tinkarar karuwar mace mace da ake samu a yakin sama da watanni shida.

Batun wa zai iya ko ya kamata ya gudanar da bincike, har yanzu shi ne abin tambaya.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG