Mafi akasarin mawakan kasar Amurka “Rappers” kan shiga cikin halin ha’ula’I, a lokutta da dama, hakan kuwa na samo asali ne a dalilin wasu sababbin rayuwa da sukan daukarma kansu na karya. Hakan yakan sa su dinga ganin kamar sun mallaki duk abun da ake bukata a duniya.
Wanda daga bisani kuwa sai labari ya canza, mafi akasarin su, suna daukar dabi’un kin biyan haraji, hakan yakan dawo ya fara bibiyar duk abun da suka tara, kana idan basu yi hankali ba, sai sun koma kamar yadda suka fara.
Binciken da muka gabatar ya bayyanar da wasu mawaka, da suka samu abun duniya, amma daga baya sai sun baka tausayi. Mawaki Lil Wayne, wanda ya mallaki kimanin sama da dallar Amurka milliyan daya $1M, yana da jirgin sama na kanshi, amma a yau abun sai a hankali.
Mawaki Tyga, wanda tsabar kudi yasa aka dibo mishi kasa daga kasar Egypt, don ya kawatar da shagon shi, amma sai ga gwamnati ta sami shi tarar sama da dallar Amurka milliyan dari $100M, na haraji. Haka mawaki Busta Rhymes, shima ya tsiyace bashi da komai, wanda a baya yayi tashe da wakar shi ta “Dangerous”