Hukumar yaki da fataucin mutane NAPTIP, shirar kano, ta ceto, wasu mutane hamsin da bakwai wadanda aka yi safararsu akan hanyarsu ta zuwa kasar Libiya.
Shugaban hukumar ta shiyar Kano, Mr Shehu Umar, a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, yace wadanna mutane sun rabu kashi biyu ne. an kuma datse su ne a kan iyakar Kongolom, a karamar hukumar Mai Adu’a, dake cikin jihar Katsina, a kan hanyarsu ta zuwa kasar Libiya.
Hukumar shige da fice ne ta cafke su ta kuma damka su ga hukumar yaki da fataucin mutane .
Su dai wadannan mutane sun biya kudaden ne da suka kama daga Naira dubu biyar zuwa Naira dubu dari biyu da hamsin ga masu safararsu.
Wadanda aka ceton shekarunsu sun kama daga goma sha biyu zuwa talatin da takwas ne,sun kuma fito ne daga jihohin Abia, Bayelsa, Delta, Edo, Enugu, Imo, Kogi Legas da kuma Ondo, kuma babu wanda ke dauke da wata takardan shedar tafiya.
Kawo yanzu dai hukumar shirya Kano ta ceto mutane dari biyu da sittin da ukku, daga farkon shekarar nan kawo yanzu, a ciki dari da saba’in da ukku, mata ne, tasa’in maza.