Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Kwamitin Majalisar Wakilai Ya Amince A Fitar Da Takardar 'Yan Democrat


Shugaba Donald Trump tare da Darektan Hukumar FBI, Christopher Wray.
Shugaba Donald Trump tare da Darektan Hukumar FBI, Christopher Wray.

Yanzu haka fadar shugaban Amurka ta WHite House ita ce zata yanke hukumci kan takardar ‘yan jam’iyyar Democrat dake karyata takardar ‘yan Republican da aka fitar, wadda ta yi zargin cewa jami’an hukumar binciken aikata laifuffuka ta FBI sun wuce makidi da rawa wajen amfani da ikonsu a lokacin da suke binciken katsalandar din Rasha a zaben 2016 na shugaban kasa.

A wata kuri’a ta bai daya, 'yan jam'iyyar Republican da na Democrat a Kwamitin Sa Ido Kan Ayyukan Leken Asiri a majalisar wakilai ta tarayya, sun amince jiya Litinin a fitar da rahoton dake nuna hanyoyin da aka yi amfani da su wajen neman iznin kotu domin sanya ido da kunnuwa a kan Carter Page, tsohon mai baiwa kwamitin yakin neman zaben Trump shawara, da ake zargi da tuntubar Rasha.

Dole sai gwamnatin Trump ta amince da fitar da takardar ‘yan Democrat daga rukunin bayanan sirri kafin a gabatar da ita ga jama’a. Ita ma takardar ‘yan Rupublican sai da ta bi irin wadannan matakai kafin a amince da fitar da ita ranar Jumma’ar da ta gabata, wadda ta janyo muhawara a fadin Washington kan rawar da siyasa ke takawa akan babbar hukumar shari’a ta kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG