Dan majalisar Jerrold Nadler ya bayyana a martanin da ya mayar kan kasidar da ta mamaye harkokin siyasar Amurka wannan makon cewa, kasidar da kwamitin tattarra bayanan sirri na majalisar dokokin ya fitar abin takaici ne, kuma ya kamata 'yan jam'iyar Republian a majalisa su ji kunya.
Takardar da Nadler ya rubutawa abokan aikinsa 'yan jam'iyar Democrt mai shafi shida, da tashoshin watsa labarai na talabijin suka samu, tace kasidar da ake kira Kasidar Nunes da shugaban kwamitin tattara bayanan sirri na majalisa da Devin Nunes na jam'iyar Republican ke jagoranta, an rubutata ne da gangan da nufin badda hankalin jama'a kuma tana cike da kurakurai.
Fitar da kasidar ya kara zafafa takun saka tsakanin Trump da abokan tafiyarsa 'yan jam'iyar Republican a majalisa a daya bangaren, da kuma 'yan jam'iyar Democrat da manyan jami'an hukumar binciken manyan laifuka ta FBI a daya bangaren, kan ko an sa siyasa a binciken katsalandan da ake zargin Rasha da yi a zaben shugaban kasar Amurka.
Facebook Forum