Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zargin Siyasa A Hukumar Bincike Ta FBI: Shugaban Hukumar Ya Ba Jami'ansa Hakuri


Shugaban Hukumar FBI Christopher Wray
Shugaban Hukumar FBI Christopher Wray

Yayin da ake ta cece-ku-ce, tun bayan bullar takardar zargin hukumar binciken Amurka ta FBI da nuna goyon baya ga jam'iyyar Demokarat a binciken zargin cewa kasar Rasha ta yi katsalandan a zaben Shugaban kasar Amurka, Shugaban hukumar ya shiga karfafa gwiwar jami'ansa. Tambaya: Shin yaya ku ke ganin za ta kaya a wannan rikicin tsakanin Trump a gefe guda da kuma hukumar bincike a daya gefen?

Shugaban Hukumar Bincike ta FBI Christopher Wray, ya gaya ma ma’aikatan hukumar jiya Jumma’a cewa ya na tare da su, bayan fitowar wata takarda, wadda ta zayyana zarge-zargen da ‘yan jam’iyyar Republican a Majalisar Dokokin Amurka ke wa hukumar ta FBI, na amfani da mukamin gwamnati ba bisa ka’ida ba, game da yadda ta ke binciken zargin da ake na cewa kasar Rasha ta yi katsalandan a zaben Shugaban kasar Amurka.

“Ina kan bakata game da kudurin nan namu na aiki ba tare da an ma na katsalandan ba, kuma kamar yadda aka gindaya a rubuce,” a cewar Wray ga ma’aikatan Hukumar ta FBI su wajen 34,000.

Wasikar karfafa gwiwar da Wray ya rubuta ma ma’aikatan na FBI ba ta ambaci takardar zargin da ta fito jiya Jumma’a ba. Bai kuma nuna alamar zai bar hukumar ba.

Shugaba Donald Trump ya caccaki hukumar ta FBI da kuma Ma’aikatar Shari’a jiya Jumma’a bayan fitowar takardar zargin.

Da wani dan jarida ya tambaye shi ko fitowar wannan takardar zargi alama ce cewa za a kori Mataimakin Attoni-Janar din Shari’ar Amurka Rod Rosenstein, sai Trump ya ce, “Ka bai wa kanka amsa.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG