Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgin Haya Na Rundunar Sojin Amurka Ta AFRICOM Ya Yi Hatsari A Benin


AFRICOM
AFRICOM

Ofishin jakadancin Amurka a Jamhuriyar Benin ya ba da sanarwar faduwar wani jirgi farar hula mai saukar ungulu, wanda rundunar sojan Amurka a nahiyar Afirka ta AFRICOM ke amfani da shi, domin ayyukan hadin gwiwa da dakarun kasar ta Benin a fannin kiwon lafiya.

A yammacin ranar Juma’a ne rahotanni daga jamhuriyar Benin suka ayyana cewa, wani jirgi mai saukar ungulu samfarin Sikosky, wanda na haya ne da rundunar tsaron Amurka ta AFRICOM ke aiki da shi ya rikito a wajejen kauyen Sedje Denou da ke da’irar Zè.

A ranar Asabar 11 ga watan Janairun 2025, ofishin jakadancin Amurka a Cotonou ya yi karin haske dangane da yadda abin ya wakana ta hanyar wata sanarwar da ke cewa, wani jirgi mai saukar ungulu wanda wasu fararen hula ke tukawa ya sami tangarda a sararin samaniyar wani wurin da ke wajen Cotonou.

Ba wanda ya ji rauni a sakamakon wannan hatsari.

Jirgin wanda rundunar sojan Amurka ta AFRICOM ta yi hayarsa, ana amfani da shi ne a ayyukan karfafa gwiwa wa dakarun Benin FAB a fannin jigilar maras lafiya.

Sanarwar ta kara da cewa, hulda a tsakanin AFRICOM da sojojin FAB na jamhuriyar Benin abu ne da ke gudana a karkashin wata yarjejeniyar da ke hangen karfafa ayyukan hadin gwiwa da taimakon juna.

Gidan rediyon BipRadio ya ce jirgin mai lamba N703NH ya tashi ne daga Parakou gab da wasu gyare gyaren da aka yi masa kafin ya rikito a wajejen karfe 4 da minti 10 na rana agogon kasar kuma dukkan mutane 4 da ke cikinsa sun fita ba tare da samun ko kwarzane ba.

Abin da ke karyatar da labaran da aka yi ta yadawa a kafafen sada zumunta, inda wasu ke cewa jirgin Faransa ne ya fadi dauke da sojojinta a jamhuriyar Benin.

Wannan al’amari na jirgin mai saukar ungulu ya faru ne kasa da sa’o’i 48, bayan wani harin ‘yan ta’addan da ya yi sanadin mutuwar sojan Benin 28 a yankinta da ke makwabtaka da kasashen Nijar da Burkina Faso.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG