‘Yan ta’addan sun hallaka sojojin Benin, inda suka kashe soja akalla 28.
Sai dai Kanar Faizu Gomina, mai magana da yawun rundunar sojin kasar ta Benin, ya ki ba da cikakken sakamako na askarawan da aka kashe a lokacin da yake bayani a kafar talabijin ta Benin ta ORTB.
Ya ce ‘yan ta'addan da suka afkawa bataliya ta MINADOR kusan su 200 ne, suka arce da kayan yaki masu yawa, ko da yake askarawan kasar ta Benin na can suna neman su ruwa a jallo a wannan iyakar ta Nijar, Benin da Burkina Faso.
Abin da ya sa masanin lamuran tsaro, kuma tsohon sojan kasar, Abdurahamane Idrissa Kado cewa, yanzu kasar Benin ta gano cewa ta'addanci gaskiya ne.
Ya kara da cewa dole ne Benin da Nijar su hada kai idan suna son yin nasara a wannan yankin gaban ‘yan ta'adda kasancewa wannan ya faru ne kwanaki kalilan bayan da sojojin na Nijar suka gwabza da ‘yan ta'adda a yankin Gaya na iyaka da Benin.
‘Yan Nijar da ‘yan Benin da ke kasar Nijar, sun yi kira ga hukumomin kasashen na Nijar da Benin da su hada hannunsu da zaransu domin samun nasara a kan ‘yan ta'addan da ta’addanci.
Saurai cikakken rahoto daga Harouna Mamman Bako:
Dandalin Mu Tattauna