Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zargin Ta'addanci: Hukumomin Benin Sun Maida Martani Kan Kalaman Shugaban Nijar


Shugaban kasar jamahuriyar Benin, Thomas Yayi Boni, wanda aka ba shugabancin kungiyar kasashen Afirka
Shugaban kasar jamahuriyar Benin, Thomas Yayi Boni, wanda aka ba shugabancin kungiyar kasashen Afirka

Ministan harkokin wajen Bénin ya gayyaci mukaddashiyar jakadan Nijar a Cotonou domin bayyana bacin ran gwamnatin kasarsa dangane da zargin da shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya yi na cewa mahukuntan Benin na da hannu a abin da ya kira yunkurin haddasa hargitsi a Nijar

A wata hira da talabijan RTN a ranar 25 ga watan Disamban 2024 shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya bayyana cewa kasar Faransa ta kafa sansanoni 2 a jamhuriyar Benin a Porjada Benjari da nufin bai wa ‘yan ta’adda horo sannan ya kalubalanci hukumomin Benin a game da wasu jiragemarasa matuki da ya ce sun yi oda daga waje wadanda daga bisani suka rarraba wa ‘yan ta’adda a Najeriya, Benin, Nijar, Burkina Faso da Mali da nufin haddasa tashin hankali a yankin Sahel.

To amma gwamnatin Patrice Talon ta yi watsi da wadannan zarge-zarge, mafari kenan ministan harkokin wajen Benin Shegun Bakary Adjadi ya gayyaci mukaddashiyar jakadan Nijar a ofishinsa a yammacin Litinin inda ya damka mata wata wasika zuwa ga takwaransa na Nijar dauke da bayanan dake nuna cewa Benin ba ta ji dadin wannan al’amari ba kamar yadda tashar Bip Radio mai watsa shirye-shirye a Cotonou ta ayyana.

Hukumomin na Benin sun gargadi takwarorinsu na Nijar su daina magana kan abubuwan da ba su gudanar da bincike kansu ba, ballantana su shiga zarge-zarge marasa tushe.

Sannan sun bukaci su maida hankali wajen canza yawu ta yadda za a wanzar da zaman lafiya da tsaro a yankin.

Minista Shegun ya jaddadawa mukaddashiyar jakadan ta Nijar cewa gwamnatin Benin na daukan batun sasanci da ‘dan uwanta da mahimmanci a tsakanin kasashen 2.

Wannan dambarwa na wakana a wani lokacin da ake ganin tafiya ta kama hanya a yunkurin sulhun na gwamnatin Patrice Talon da Abdourahamane Tiani don ganin Nijar ta bude iyakarta da Benin wacce ke rufe yau sama da shekara 1 sakamakon barazanar tsaron da hukumomin Nijar suka ce sun hango a bisa zargin Benin din da bai wa Faransa damar girke dakaru a kan wata mummunar manufa, abin da makwafciyar kasar ta musanta.

Kace-nace a tsakanin wadannan kasashe na yammacin Afirka wani abu da masana huldar kasa da kasa irinsu Moustapha Abdoulaye ke jan hankulan duniya cewa an kai matakin da za a fara yunkurin shiga tsakanin a kungiyance.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Hukumomin Benin Sun Maida Matani Kan Kalaman Janar Tiani Na Zargin Kasarsu Da Ta’addanci.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG