Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Najeriya Ya kirkiri Wata Sabuwar Fasahar Samar da Lantarki


INDIA
INDIA

Hukumar kula da makamashi ta duniya ta IEA, ta kiyasta cewa mutane miliyan 600 a Afrika basu da wutar lantarki. Duk da cewa Najeriya ta sami lantarki sama da karni guda da ya wuce, har yanzu ba a samun igantacciyar wutar lantarki a kasar. Amma wani dan Najeriya ya fito da wata sabuwar fasaha.

Martins Davo dan shekara 28 da haihuwa, ya na da shagon aski a Abuja kusan tsawon shekaru hudu. Amma kamar sauran daruruwan masu sana’o’i irin wannan, shagonsa bai da wutar lantarki kuma zabin amfani da janareto ya zama da tsada sosai bayan da gwamnati ta cire tallafin man fetur a shekarar da ta wuce.

"Ba mu da wuta a nan, kuma ko man da za a saya a zuba a janareto don yi wa mutane aski ya yi tsada sosai, ta yaya za ka sayi lita daya na man fetur a kan Naira 700, sannan ka ce mutane su biya Naira 200 ko 300 kudin aski?"

Martins Davo na dogaro da na’urar aski mai amfani da batir don biyan bukata, amma duk da haka ya na gwagwarmaya a sana'ar.

Najeriya na fama da karancin wutar lantarki tsawon shekaru da dama saboda rashin tabbas na manufofi da ka'idojin gwamnati, da samar da iskar gas, da rashin isassun cibiyoyin ababen more rayuwa. Hukumomin Najeriya sun ce lamarin na yin tasiri kan damar wasu ‘yan kasar miliyan 100 ta yin rayuwa mai inganci. Amma wannan kalubalen na bude hanyar sabbin kirkire-kirkire kamar ta na'urar janareton Regnault Bamiji mai makamashi mai tsafta, wadda ke da fasahar batiri mai caza kansa. Regnault ya yi imanin cewa sabuwar fasaharsa na iya taimakawa wajen magance matsalolin wutar lantarki ga Martins Davo da sauran mutane da yawa da ke fuskantar irin wannan kalubalen.

“Yadda na'urar ke aiki shi ne, ta na jan makamashi kadan daga inda makamashin yake daga nan ta ja shi zuwa ga batirin da ke jikin na’urar. Idan cajin batirin ya kare kuma babu hasken rana, ko wutar lantarki, ko ma makamashin iska don caja shi, wannan fasahar na taimakawa. Ta na caza batiri nan da nan.

Regnault Bamiji mai shekaru 61 ya kasance mai kirkire-kirkire sama da shekaru 20. Da wannan fasahar tasa ya ke amfani don samar da lantarki a gidansa, kuma a kwanan nan ya kulla kawance da wani kamfani na kasar Italiya. Kamfanin ya na taimaka masa kirkirar wata sabuwar fasaha irin wannan, kuma zasu raba ribar idan na’urar ta shiga kasuwa. Regnault ya kuma kera wata mota mai amfani da lantarki, ta hanyar amfani da irin wannan fasahar.

“A Italiya a yanzu, sun sake kera irin wannan na'urar da muke da ita a nan, amma nasu sun fi wadanda muke da su kyau, saboda kamfani ne da za mu kulla yarjejeniya da shi, a zahiri na so a ce a Afirka ko kuma a Najeriya za a yi yarjejeniyar, amma ba ni da wani zabi saboda yawan rashin yarda, ko kuma mutane ba sa son su amince da wani abu da aka yi daga cikin kasarsu.”

A cikin watan Fabrairun wannan shekarar ta 2024, ma'aikatar kere-kere ta Najeriya ta yi alkawarin tallafa wa fannin kirkire-kirkire na cikin gida don bunkasa tattalin arziki da magance matsalolin da ake da su. Duk da cewa hukumomi ba su bayyana yawan taimakon da suka yi alkawarin ba da wa ko kuma suka bayar ba, sun ce ma’aikatar za ta samar da yanayi mai kyau na tallata kayayyakin da aka kera a cikin gida.

Regnault Bamiji ya ce, sau da dama ya gabatar da na’urarsa ga jami'an gwamnati, amma ba su nuna sha'awa ko goyon baya ba. Ya ce idan har hukumomi ba su cika alkawuran da suka dauka ba, igantacciyar wutar lantarki mai rahusa za ta gagari miliyoyin ‘yan Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG