Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yajin Aikin Gama-Garin Da Kungiyoyin Kwadago Suka Shiga Ya Shafi Harkokin Kasuwanci, Filayen Jiragen Sama, Asibitoci Da Samarda Lantarki


Strike
Strike

Duk da shigowar da Majalisar Tarayya tayi cikin zance a kurarren lokaci domin kaucewa shiga yajin aikin da aka ayyana a Juma’ar data gabata, tattaunawar ta cije, abinda ya kai ga fara yajin aikin.

Ma’aikata sun kauracewa wuraren aiki a fadin Najeriya sakamakon yajin aikin da kungiyar kwadago ta NLC da takwararta ta TUC suka tsunduma sakamakon karin kudin lantarki da kuma rashin cimma matsaya kan batun mafi karancin albashi.

Yajin aikin ya kassara harkokin kasuwanci da muhimman ayyuka a fadin Najeriya ciki harda makarantu da asibitoci da samarda wutar lantarki sakamakon biyayyar da ma’aikatan suka yi da umarnin kungiyoyin kwadagon nlc da tuc.

Tun daga jihar Rivers dake shiyar kudu masu kudanci zuwa Kaduna dake shiyar arewa maso yammacin Najeriya, ma’aikatan sun kassara harkokin tattalin arziki.

Al’amura sun tsaya cik a tashoshin jiragen saman Najeriya ciki harda na Abuja, Fatakwal, Kaduna da Legas.

Filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa dake Abuja
Filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa dake Abuja

Haka kuma, harkokin koyo da koyarwa a makarantun sun tsaya a fadin kasar, an maido da daliban da suka riga suka isa makarantu zuwa gida.

GDSS Abuja
GDSS Abuja

Shugabannin kwadago a jihar Kaduna sun rufe babbar kofar shiga asibitin masu larurar kunne na kasa. Inda suka tarwatsa ma’aikata tare da hana marasa lafiyar dake wajen asibitin shiga cikinsa.

Da sanyin safiyar yau Litinin, ma’aikata suka rufe babbar tashar samarda lantarki ta kasa, inda suka jefar kasar cikin duhu.

Filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa dake Fatakwal
Filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa dake Fatakwal

A bisa biyayya da umarnin kungiyoyin kwadago na nlc da tuc, Kungiyar Ma’aikatan Bangaren Lantarkin Najeriya (NUEE) sun rufe sashen ayyuka na kamfanin rarraba hasken lantarki na Kaduna (KAEDCO)

Shugaban reshen jihar Kaduna na kungiyar kwadago ta tuc, Abdullahi Danfulani, yace dukkanin rassan kungiyoyinsu na biyayya ga yajin aikin kuma baza su tsahirta ba har sai gwamnatin tarayya tayi abinda ya dace.

Haka kuma kungiyoyin kwadagon sun rurrufe ofisoshin gwamnati tare da kawo tsaiko a hada-hadar wasu bankuna.

A jihar Edo kuma, kungiyoyin kwadagon nlc da tuc din sun rufe sakatariyar gwamnatin jihar dake birnin Benin, inda suka hana ma’aikata shiga ciki.

Haka al’amarin ya kasance a jihohin Legas, Ogun, Oyo da Rivers.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG