Sakamakon umarnin ragin kudin lantarkin da Hukumar Kayyade Farashin Lantarki ta Najeriya (NERC) tayi wa kwastomominta dake kan tsarin “Band A” na masu samun wuta akalla tsawon sa’o’i 20 a watan Mayun da muke, Kamfanin Rarraba Hasken Lantarki na Ikeja, ya sanarda rage kudin wuta ga abokan huldarsa dake kan “Band A” daga Naira 225 kan kowace kilowatt zuwa Naira 206 da kwabo 80.
Da yake tabbatar da biyayyarsu ga umarnin ragin kudin wutar, Shugaban Sashen Hulda da Jama’a na Kamfanin Rarraba Lantarki na Ikeja, Kingsley Okotie, yace “muna biyayya ga dukkanin umarnin da NERC ta bayar don mun san hakan ne mafi alkhairi ga kowa. Muna baiwa abokan huldarmu tabbacin cigaba da inganta ayyukanmu a kokarin da muke yi na kyautata musu.”
Sanarwar da kamfanin rarraba hasken lantarki na Ikeja ya fitar, wacce jaridar The Nation ta samu kwafe tace: “muna sanar daku game ragin kudin wutar da muka yiwa kwastomomin dake kan layinmu na “Band A” daga naira 225 zuwa 206.80 akan kowace kilowat tun daga ranar 6 ga watan mayun da muke ciki tare da tabbacin samun wuta ta tsakanin sa’o’i 20 zuwa 24 a kowace rana. Kudin wutar da ake cazar abokan huldarmu dak e kan layukan Band B, C, D, da E na nan bai sauya ba.
A baya, sanarwar karin kudin wutar da aka yiwa kwastomin dake kan layin “Band A” a ranar 3 ga watan Afrilun daya gabata, ta ci karo da suka daga ‘yan Najeriya. Ko a makon daya gabata ma, sai da Majalisar Wakilai ta umarci Hukumar nerc ta sakee nazarin game da karin.
Dandalin Mu Tattauna