A yayin da ‘yan Najeriya ke kara matsin lamba ga gwamnati a kan kudurori da suka ce yana kuntatawa ‘yan kasa, wasu ‘yan kasuwa da masu sharhi a kan al’amurran yau da kullum sun ce rage farashin kudin wutan wadanda ke kan tsarin ‘Band A’ ba zai yi tasiri ga yanayin matsin da aka jefa ‘yan kasa a ciki ba, kuma kamata ya yi ana daukan matakan da suka dace kafin fitar da kuduri ga kasa.
Rahotanni dai sun yi nuni da cewa matakin da kamfanin Ikeja electric ya fitar ya biyo umarnin da gwamnatin kasar ta bayar na amincewa da batun rage farashin wutar ga kwastomomin dake karkashin tsarin Band A biyo bayan kiraye kirayen da ‘yan kasa suka yi tun ranar 4 ga watan Afrilu da tsarin ya fara aiki.
Wannan lamarin dai ya sanya ‘yan Najeriya cikin wani yanayin matsi kuma rage kudin wutan lantarkin da aka yi ba wani tasirin da zai yi kamar yadda fitacciyar ‘yar kasuwa kuma mazauniyar birnin tarayya Abuja, Hajiya Aisha Abubakar ta fada.
Mai Sharhi a kan al’amurran yau da kullum, Ibrahim Hussain Abdulkarim ya ce a fitar da mataki a janye da gwamnatin nan ta dauki salonsa ba abu ne mai kyau ba ganin irin barnar da ake tafkawa da kudurorin da aka yi ta bullo da su na baya-bayan nan.
A wani bangare kuwa masanin tattalin arziki, Mallam Kasim Garba Kurfi ya ce ragin da aka yi bai taka kara ya karya ba kuma kamata ya yi gwamnati ta kara Ninka kokari wajen kawo wa al’umma sauki.
Idan ana iya tunawa, a farko-farkon watan Afrilun da ta gabata ne gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ta amince da karin kudin wutan lantarki a kan Naira 225 killowatt 1 a sa’a 1 ga masu amfani da wutar lantarki na Band A a kasar.
Matakin da daga bisani ya haifar da rudani a cikin kasar inda kungiyoyin fararen hula da sauran ‘yan Najeriya suka bayyana matakin a matsayin na kara matsi ga matsalar tattalin arzikin da ‘yan kasa ke ciki.
A saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:
Dandalin Mu Tattauna