Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tillerson Ya Ce Amurka Zata Gina Dangantaka Mai Karfi Da Kasashen Afirka


 Rex Tillerson , Sakataren Harkokin Wajen Amurka.
Rex Tillerson , Sakataren Harkokin Wajen Amurka.

Yayinda ya rage masa sa'o'i kadan ya fara ziyarar wasu kasashen Afirka, Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya zargi kasar China da son maida kasashen Afirka masu dogaro da ita sai ya kara da cewa Amurka zata karfafa dangantakarta da kasashen

'Yan sa'o'i kadan kafin ya fara rangadin aikinsa na farko a nahiyar Afirka, sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, yace Amurka ta kuduri aniyar gina harsashin dangantaka mai karfi a tsakaninta da Afirka, yana mai zargin kasar China da laifin karfafa akidar sanya kasashe su zamo masu dogara da ita a irin huldar da take yi da nahiyar.

A cikin jawabin da ya gabatar dake bayyana manufofin gwamnatin shugaba Trump na yin hulda da kasashen Afirka, Tillerson yace Amurka tana kwadayin saukar da shingayen cinikayya da zuba jari a Afirka, nahiyar da a yanzu babbar abokiyar cinikayyarta ita ce kasar China.

Sakataren harkokin wajen ya kara da cewa manufar Amurka ta karfafa gudanar da mulki na kwarai a nahiyar, ta sha bambam da manufar China dake karfafa "dogaro, da kwantaraki na ha'inci, da rancen neman cutarwa da zarmiya da cin hanci wadanda ke sanya kasashe shiga cikin ukubar bashi da tauye musu diyauci."

Wannan ziyara tana zuwa watanni biyu a bayan da shugaba Trump ya haddasa tankiya da musanyar zafafan kalamu a lokacin da ya bayyana kasashen Afirka da wata kalma ta kaskanci lokacin taronw asu sanatoci a ofishinsa. Kungiyar Tarayyar Afirka mai wakilai 55, ta nemi da shugaban ya nemi gafara. Wasu jakadun kasashen Afirka a MDD ma sun yi tur da kalamun na Trump.

Har yanzu shugaba Trump bai zabi babban jami'in diflomasiyyar da zai kula da huldar Amurka da kasashen Afirka ba, shekara guda da wani abu bayan hawarsa kan mulki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG