Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Amince Ya Gana Da Shugaba Kim Jong Un Na Koriya Ta Arewa


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

A wani al'amari na bazata, Shugaban Amurka Donald Trump ya amince ya gana da mutumin da su ka yi ta musayar zafafan kalamai da shi, wato Shugab Koriya Ta Arewa. Amma wasu na yabawa wasu kuma na shakka.

An yi kaffa-kaffa da lale da kuma waswasi, bayan amincewar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ba-zato ba-tsammani, ta ya gana da Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un zuwa watan Mayu a birnin Pyongyang, don su tattauna kan yadda za a kawo karshen shirin makaman nukiliyar Koriya Ta Arewa.

Chung Eui-yong, Shugaban Hukumar Tsaron Kasa ta Koriya Ta Kudu ne ya bayar da sanarwar cimma wannan yarjajjeniyar da daren jiya Alhamis. Ya zo nan birnin Washington musamman don ya yi bayani ga Trump da jami’an Fadar White House ciki har da Mai Bayar Da Shawara Kan Harkokin Tsaron Kasa H.R. McMaster, kan irin cigaban da aka samu a diflomasiyyance lokacin da ya je birnin Pyongyang a farkon wannan satin. Ya kuma isar da sakon kayyata ta baka, da Shugaban Koriya Ta Arewar ya yi ma Shugaban na Amurka.

“Shugaba Trump ya yi lale da wannan bayani kuma ya ce zai gana da Kim Jong Un zuwa watan Mayu don a cimma yarjajjeniyar dindindin ta kawo karshen shirinsa na nukiliya,” a cewar Chung.

Chung dai ya jagoranci wata tawagar jami’an diflomasiyyar Koriya Ta Kudu da ta gana da Shugaban na Koriya Ta Arewa a birnin Pyongyang ranar Litini. Daga bisani, ya isar da sakon Shugaba Kim na aniyarsa ta tattaunawa da Amurka game da batun kawo karshen shirinsa na nukiliya, da kuma alkawarinsa na daina gwaje-gwajen makaman nukiliya da makamai masu linzami yayin da ake shirin fara tataunawar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG