Bashir Dan Malam shugaban dilalan sayar da man Fetur ko IPMAN a takaice yace su da wasu jami'ai sun kafa wani kwamiti dake zagayawa domin tabbatar an sayar da man fetur kan farashin da aka kayyade.
Dangane da karancin man fetur din Bashir Dan Malam yace al'amari ne na gwamnati. Yace su idan an basu zasu dauka. Motocinsu suna Legas suna jira a basu man su dauka. To saidai karancin man ya sa farashinsa ya yi tashin goron zabi musamman a kasuwar bayan fagge kodayake su ma din sun koka da farashin da suke samunsa.
Sagir Hassan daya daga cikin masu sayar da man a gefen titin zuwa gidan dabbobi a Kano yace suna sayarda lita daya nera dari da talatin da biyar. Yace matsalar ita ce kullum kara kudin mai suke yi. Yanzu suna sayarda galan daya nera dari bakwai domin suna samun wahala wurin samun man.
Yanzu sabili da wuyar samun man mutane suna tururuwa su samun kadan su sa cikin ababen hawansu. Masu kasuwar bayan fagge yanzu ne kakarsu ta yanke saka kodayake in ji Hassan ribar da suke samu yanzu ta ragu.
Alhaji Suleiman Abubakar kwanturolan jihar Kano na GPR yace mai na isa duk tashoshin mai kuma ana sayarwa kan farashin da gwamnati ta amince. Yace a cikin Kano a na sayarwa yadda aka kayyade saidai a kauyuka farashin ka iya banbanta domin babu yadda za'a yi su kasance koina a kowane lokaci.
Tuni dai masu motocin sufuri suka yi karin kudi da suke karba daga hannun fasinjoji. Farshin nasu ya haura da kimanin kashi ashirin cikin dari.
Ga karin bayani.