Gwamnatin tarayya ta musanta cewa tana shirin kara farashin mai, dalili da yasa masu fataucin mai suka kara farashin mai. Wannan yana daga cikin karin dalilai da suka janyo karancin mai musmaman a biranen Kano da Legas.
Da yake karyata wannan jita jita wani kakakin kamfanin mai na Najeriya Umar Farouk yace a safiyar talatan nan kamfanin ya bada ton dubu 25 na mai ga dillalan mai, kuma ya bayyana fatar zuwa karshen wannan mako za'a sami sauki wannan batu.
Shima da yake magana kan dalilan da suka janyo karancin mai, wani dillali mai zaman kansa a kano, karkashin inuwar kungiyar dillalan mai da ake kira IPMAN, komorade Alhassan Uba Idris, yace babbar matsalar itace harkar mai baki dayansa ba a gudanar da shi kan gaskiya.
Yace shigo da mai daga ketare harka ce da ake yi zangon watanni uku-uku, kuma zangon farko a wannan shekara ba a tashi bada kwangilar kawo mai ba sai cikin makon jiya.
Masu abeban hawa a kano da legas sun bayyana irin hali da suke ciki.
Ga Karin bayani.
Masu abubuwan hawa a kano suna shafe sa'o'i masu yawa a layi suna neman mai.
WASHINGTON, D.C. —