Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Fuskantar Hauhawar Farashin Kayan Masarufi A Jamhuriyar Nijar


‘Yan Nijar Na Kokawa A Game Da Tashin Farashin Kayayyakin Masarufi
‘Yan Nijar Na Kokawa A Game Da Tashin Farashin Kayayyakin Masarufi

Farashin kayayyakin abinci ya yi tashin gwauron zabi a birnin Agadas da ke arewacin Nijar kwanaki kalilan bayan da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta kakaba takunkumin karya tattalin arziki ga kasar.

Kwanaki kalilan bayan da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO ta sanya takunkumin karya tattalin arziki kan Jamhuriyar Nijar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi, farashin kayayyakin bukatun yau da kullum ya yi tashin gwauron zabi, lamarin da ya sa al’ummar Nijar musamman na jihar Agadas da ke arewacin kasar shiga cikin mawuyacin hali sakamakon karancin kudi da suke fama da shi.

Kafin kungiyar CEDEAO ta kakaba wa Nijar takunkumin, 'yan kasar na sayen buhun shinkafa a kan kudi CFA 10,000, amma a yanzu farashin yana hauhawa inda a wasu wurare ake sayen shinkafar a kan kudi CFA 16,000.

Kayayyakin Masarufi ya fara tashi a Nijar
Kayayyakin Masarufi ya fara tashi a Nijar

A halin gaskiya, kusan farashin dukkanin kayayyakin bukatun yau da kullum na ci gaba da hauhawa sakamakon yadda 'yan kasuwa ke boye hajarsu domin samun kazamar riba.

‘Yan Nijar Na Kokawa A Game Da Tashin Farashin Kayayyakin Masarufi
‘Yan Nijar Na Kokawa A Game Da Tashin Farashin Kayayyakin Masarufi

Tuni dai kananan 'yan kasuwa suka shiga cikin halin zullumi musamman bayan da suka fahimci halin tsaka mai wuya da zasu tsinci kansu a ciki.

Musa Sabitu, shi ne shugaban kananan 'yan kasuwa a Agadas, ya ce kananan 'yan kasuwarsu sun fi zuwa Najeriya domin saro kayayyaki amma rufe iyakar da aka yi bayan da wasu sojojin kasar suka kifar da gwamnati shugaba Mohammed Bazoum ya kawo musu cikas.

Masana harkar tattalin arziki irinsu Mamman Sani, na ganin wannan matsalar zata shafi talaka ta kuma nakasa tattalin arzikin Nijar.

Dama Nijar ta dogara ne da Najeriya da Jamhuriyar Benin wajen shigo da kayanta na bukatun yau da kullum.

Saurari rahoton Hamid Mahmoud cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG