Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Sanar Da Majalisa Shirin ECOWAS Na Tura Dakaru Nijar


Dakarun Najeriya
Dakarun Najeriya

Najeriya tuni ta katse bai wa kasar ta Nijar wutar lantarki da shige da ficen kayyaki.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da Majalisar Dokokin kasar jerin matakan da kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS ke dauka bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar.

Daga cikin matakan har da shirin da ECOWAS ke yi na tura dakaru zuwa Nijar idan hakan ya zama dole.

A ranar 26 sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasa suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum tare da tsare shi.

Jim kadan bayan juyin mulkin kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS ta kakabawa kasar takunkumai.

Najeriya tuni ta katse bai wa kasar ta Nijar wutar lantarki da shige da ficen kayyaki.

An kuma dakatar da safarar kayayyaki zuwa kasar, lamarin da rahotanni suka ce ya haifar da hauhawar farashin kayan masarufi.

ECOWAS da kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da Majalisar Dinkin Duniya da kasashe irinsu Amurka, sun bukaci sojoji da su maido da gwamnatin Bazoum su kuma koma barikin soja.

Amma ga dukkan alamu sojojin sun yi kememe sun ki bin umurnin.

A ranar Alhamis Tinubu wanda shi ne shugaban kungiyar ta ECOWAS, ya tura wata tawaga karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Abdulsalam Abubakar da Sarkin Musulmi Muhammad Abubakar Sa’ad III don su shiga tsakani.

Amma tawagar ta koma gida ba tare da ganawa da jagoran juyin mulkin Janar Abdourahame Tchiani ba da Shugaba Bazoum.

Ma'aikatar tsaron Najeriya a ranar Alhamis ta ce har yanzu ba a ba ta umurnin tura dakaru Nijar ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG