Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Napoli Ta Lashe Gasar Seria-A Ta Italiya


FBL-ITA-SERIEA-TORINO-NAPOLI
FBL-ITA-SERIEA-TORINO-NAPOLI

Dan wasan Najeriya Victor Osimhen ya zura kwallo a raga yayin da kungiyar Napoli ta lashe Seria-A ta farko cikin shekaru 33 bayan ta tashi 1-1 da kungiyar Udinese da daren ranar Alhamis.

Sandi Lovric ne ya zura wa Udinese kwallo a minti na 13 da fara wasan yayin da Osimhen ya rama wa Napoli a minti na 52 da fara wasa a rabin lokaci na biyu.

Dan wasan mai shekaru 24 da haihuwa a yanzu ya zama dan wasan Afirka da ya fi cin kwallaye a gasar Seria A guda.

Ya kuma karya tarihin Samuel Eto’o na Kamaru na wanda ya fi yawan cin kwallaye a cikin 'yan wasan Afirka, inda ya ci kwallo a kakar gasar Seria-A guda daya da kwallaye 22.

Magoya bayan Napoli suna murna bayan lashe gasar Seria A ta Italiya, 05-04-23
Magoya bayan Napoli suna murna bayan lashe gasar Seria A ta Italiya, 05-04-23

Napoli ta lashe gasar Seria-A ta karshe a shekarar 1990.

Osimhen, Kvaratskhelia, da sauran yan wasan Spalletti sun fada tarihin Napoli. Watakila ba za su taba kafa tarihi irin na El Diego Maradona ba, amma har abada za su rike wuri na musamman a zukatan magoya bayan Azzurri, wadanda rabon su yi bikin samun wani matsayi haka tun cen wajen1990.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG