ABUJA, NIGERIA - Sanata Remi wacce ta ba da Naira 250,000 ga kowace bazawara har su 1, 709 ta ce ta yi hakan ne da fatan za su jujjuya kudin a matsayin jari don tallafawa rayuwar marayun da aka bar masu.
Yayin kuma da ta ke jinjina ga mayakan da suka rasa rayukansu wajen kare kasa Najeriya, uwargidan shugaban kasar ta ce akwai nauyin da ya rataya a wuyan mahukunta na kula da walwalar mata da marayun da aka bari.
Ta kara da cewa kasancewar matar soja ba karamin gwagwarmaya ba ne ganin hakan cike ya ke da tarabbabi, fargaba da ma sadaukarwa.
Da yake jawabi, babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron Najeriyar, Janaral Christopher Musa ya godewa matar shugaban Najeriyar bisa wannan gudunmawar.
Ya ce hakan zai taimaka gaya wajen karfafawa sauran matan da a halin yanzu mazajensu ke raye kuma a bakin aiki.
Janar C.G Musa ya kara da cewa wannan ya gwada cewa irin gagarumar sadaukarwar da mayakan sukai na rasa rayukansu bai tafi a banza ba.
Baki daya jimlar kudi Naira miliyan 425,000.000 uwargidan shugaban kasar ta rabawa zawarawa da marayun na sojoji.
Dandalin Mu Tattauna