Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Ceto Karin 'Yan Matan Chibok


TSOHON HOTO - Wasu iyaye lokacin da suka hadu da 'yarsu lokacin da Boko Haram ta sako 'yan mata 82 a 2017.
TSOHON HOTO - Wasu iyaye lokacin da suka hadu da 'yarsu lokacin da Boko Haram ta sako 'yan mata 82 a 2017.

Bayan kimanin shekara bakwai da kungiyar Boko Haram ta sace su, rahotanni na cewa wasu daga cikin ‘yan matan makarantar sakandare ta Chibok da suka rage a hannun kungiyar sun samu kubuta.

Rahotanni dake fitowa daga arewa maso gabashin Najeriyar na cewa ‘yan matan na Chibok da suka samu kubuta yanzu, su na daga cikin mutane da yawa da sojojin kasar da suke yaki da mayakan Boko Haram a dajin Sambisa suka kubutar kwanan nan.

Jagoran al’ummar Chibok a Abuja, Hosea Sambido ya shaidawa Muryar Amurka cewa sun yi farin ciki da labarin kubutar da karin wasu ‘yan matan na Chibok.

“Har yanzu dai ba mu samu cikakken bayani a game wannan lamari ba, domin har yanzu mutanen dake Chibok su ma labarin kawai suka ji. Sannan ‘yan jarida da suka bayar da labarin, sun ce sojoji ba su ba su cikakken labarin ba”, a cewar Sambido.

Sambido ya kara da cewa “labarin da muke da shi, shi ne sojoji sun fafata da mayakan Boko Haram a dajin Sambisa, kuma sun samu kubutar da mutane da yawa daga hannun Boko Haram, ciki har da ‘yan matan Chibok.”

Jami'an gwamnatin Najeriya suna ganawa da 'yan matan Chibok su 21 da aka sako alhamis 13 Oktoba,m 2016 a Abuja
Jami'an gwamnatin Najeriya suna ganawa da 'yan matan Chibok su 21 da aka sako alhamis 13 Oktoba,m 2016 a Abuja

“Har yanzu ba mu san ko su nawa ne ba, ko kuma su wanene ba. Amma mu na da kyakkyawar fata akwai ‘yan matan Chibok a cikinsu”, a cewar Sambido.

Har yanzu dai rundunar sojin Najeriya ba ta yi karin bayani ba a hukumance.

Sojojin kasar da hadin gwiwar dakarun kawance na yankin tafkin Chadi su na ci gaba da dannawa cikin dajin Sambisa, inda suke ci gaba da fatattakar mayakan Boko Haram.

Wata majiyar tsaro ta shaidawa Muryar Amurka cewa sojojin Najeriya na ci gaba da lalata sansanonin Boko Haram tare kuma da kashe mayakan kungiyar da dama a cikin dajin na Sambisa.

A shekarar 2014 ne mayakan Boko Haram suka kai hari makarantar sakandare ta mata dake Chibok a jihar Borno, inda suka sace dalibai ‘yan mata 276.

Lamarin ya sa kasashen duniya suka yi ta Allah wadai da sace ‘yan matan, abin da ya kai ga kaddamar da wani yunkuri na ganin an ceto su da ake wa lakabi da #BringBackOurGirls.

Masu gangamin ganin an ceto 'yan matan Chibok a 2016
Masu gangamin ganin an ceto 'yan matan Chibok a 2016

Wasu daga cikin ‘yan matan sun samu tserewa a lokacin da aka sace su. An kuma sake gano wata guda daga cikin ‘yan matan a watan Mayun 2016 lokacin da a ka same ta a cikin daji ta na neman a taimake ta.

A shekarar 2016, kungiyar ta Boko Haram ta sako 21 daga cikin ‘yan matan bayan wata tattaunawa da gwamnatin Najeriya.

'Yan matan Chibok da Boko Haram ta sace
'Yan matan Chibok da Boko Haram ta sace

Sannan a shekarar 2017, kungiyar ta sako ‘yan matan 82 a wata musayar fursina da gwamnatin Najeriya.

Tun bayan nan, ba a sake jin duriyar sauran ‘yan matan 112 da suka rage a hannun kungiyar ta Boko Haram ba.

Karin bayani akan: ​Chibok, Boko Haram​, Nigeria, da Najeriya.​

XS
SM
MD
LG