Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Bada Tallafin Kusan Dala Miliyan 104 Saboda Rikicin da ke faruwa A Najeriya


Hukumar Raya Kasashe Masu Tasowa ta Amurka (USAID) za ba da kusan dala miliyan 104 a matsayin karin taimakon jinkai don magance matsalolin da ke faruwa a Najeriya, inda kimanin mutane miliyan 8.7 ke cikin hadari.

Wannan ƙarin taimakon zai samar da tallafi da ake buƙata cikin gaggawa ga al'ummomi, haɗe da abinci, kiwon lafiya, abinci mai gina jiki, matsuguni, kariya, tsabtataccen ruwa, tsabtataccen jiki, da shirye-shiryen haɗin gwiwa na jama'a.

Tun daga shekara ta 2015, tashin hankali da rashin tsaro sun kori mutane daga gidajensu kuma sun sanya bukatun agaji na jinkai sun karu a Arewacin Najeriya.

Annobar COVID-19 ta dada haifar da matsalar rashin abinci, wadda ta haifar da damuwa kan yadda za a iya kare mutane, ciki har da tashin hankalin da ya shafi jinsi, da rashin isasshiyar damar samun abubuwan bukata kamar tsabtataccen ruwan sha, abinci mai gina jiki, da kuma matsuguni.

Kasar Amurka ita ce kasa daya da ta fi bayar da tallafi don ayyukan jinkai a Najeriya, bayan da ta samar da kusan dala miliyan 505 a cikin Kasafin Kudin shekarar 2020 da 2021. Amurka na nan kan bakarta ta taimaka wa mutanen da wannan rikici ya shafa kuma za ta ci gaba da bayar da muhimmin tallafi ga mutanen Najeriya.

Kasar Amurka ta yi kira ga sauran masu hannu da shuni da su hada hannu wajen samar da taimakon ceton rai ga ‘yan Nijeriya wadda ke cikin mawuyacin hali da ma al’ummomin da ke karbar su.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG