Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta zabi Sanata Iyorchia Ayu a matsayin shugaban jam’iyya na kasa.
Jam’iyyar ta zabi Ayu ne a lokacin babban taronta na kasa da ta gudanar a Abuja inda ya tsaya takarar shi kadai ba tare da abokin hamayya ba.
Wakilai sama da 3,000 daga sassan Najeriya suka halarci babban taron don zaben jami’an da za su tafiyar da ramagar jam’iyyar a matakai daban-daban.
Ana sanar da shi a matsayin sabon shugaban jam’iyyar, Ayu wanda ya taba rike mukamin shugaban majalisar dattawa, ya mike ya hau dandalin magana don yin jawabin.
“A lokacin da muka fara wannan tafiyar shekaru 23 zuwa 24 da suka gabata, ba mu taba tunanin za mu kai ga wannan matsayi ba – inda muka yi mulki har tsawon shekaru 16.
“Mun fuskanci kalulabe a baya, amma ga duk wanda yake so ya sani, PDP ta dawo – PDP ta dawo don ta ceto Najeriya daga kangin da muka shiga cikin shekaru shida.” Ayu ya ce.
Kazalika taron na PDP wanda ya faro daga ranar Asabar zuwa wayewar garin Lahadi, ya zabi Ambasada Umar Damagum a matsayin mataimakin shugaban jam’iyya shiyyar arewacin Najeriya.
Sai Taofeek Arapaja wanda ya aka zaba a matsayin mataimakin jam’iyya shiyyar kudancin Najeriya.
An kuma zabi Samuel Anyanwu a matsayin Sakataren jam’iyya na kasa sai Ahmed Mohammed a matsayin ma’aji na kasa.
An kuma zabi Mohammed Kadade Suleiman a matsayin shugaban matasan jam’iyyar na kasa.
Ana iya sauraran rahoton wakilin mu Nasiru Adamu El-Hikaya, a cikin sauti.