Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arewaci Da Kudancin Sudan Sun Amince Su Janye Haramtattun Sojoji


Shugaban Sudan Omar al-Bashir.
Shugaban Sudan Omar al-Bashir.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kudanci da arewacin Sudan sun amince su janye haramtattun dakarunsu daga yankin Abyei mai arzikin man fetur da ake takaddama a kai daga yau Talata.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kudanci da arewacin Sudan sun amince su janye haramtattun dakarunsu daga yankin Abyei mai arzikin man fetur da ake takaddama a kai daga yau Talata.

A wata takardar jawabin da aka gabatar ran Lahadi, Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta ce akwai kyakkyawar niyya a tattaunawar da bangarorin biyu su ka yi, kuma sun amince su ida janyewar zuwa ran 17 ga watan Mayu.

Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma ce da arewa da kudun za su yi aiki tare wajen kwantar da hankali a yankin, sannan su yi ban baki ga al’ummarsu game da yadda za a aiwatar da yarjajjeniyoyin da aka cimma tsakanin bangarorin biyu.

Baya ga janye haramtattun dakaru, yarjajjeniyoyin da aka cimma a watannin Janairu da Maris ya tanadi kafa rundunar tsaro da ‘yan sanda na hadin gwiwa da za su kunshi jami’ai daga bangarorin biyu da za a girke su a wurin.

XS
SM
MD
LG