Jakadan ƙasar Turkiyya a Nigeriya, Jakada Hidaye Bayraktar ne ke jaddada hakan yayin da ya kaiwa Babban Hafsan Hafsoshin sojojin ƙasan Nigeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ziyara a shelkwatar rundunar da ke Abuja.
Jakadan na Turkiya ya bayyana cewa dalilin ziyararsa ita ce Ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu da kuma taimakawa Najeriya wajen yaƙi da ta'addanci.
Ya ƙara da cewa ƙasashen biyu duk sun yi fama da matsalolin tsaro, ya bayyana cewa kamfanonin ƙera kayan tsaro na ƙasashen biyu sun shiga yarjejeniya domin rage ayyukan 'yan ta' adda.
A nasa jawabin, Babban Hafsan sojojin ƙasan Nigeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya bayyana ziyarar da cawa wata dama ce ta inganta dangantaka tsakanin ƙasashen musamman ma rundunar ƙasa ta ƙasar Turkiyya. Ya bayyana cewa a ziyarar sa zuwa ƙasar Turkiyya kwanan baya ya kai ziyara kamfanin sarrafa kayayyakin yaƙi na ƙasar.
Janar Yahaya ya tabbatar da cewa ziyarar Jakadan za ta ƙara danƙon zumunci tsakanin ƙasashen musamman domin ƙara himma wajen inganta kayan yaƙi da kuma musayan bayanai a tsakaninsu
In za a iya tunawa ko a makon da ya gabata ma saida Najeriya ta sa hannu a wata yarjejeniyar samarwa mayakan kasar makamai da kasar Rasha .a fadi tashin da kasar keyi na kawo karshen kalubalen tsaro da ya addabi kusan duka sassan najeriyar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: