Mutane talatin da tara da aka kashe da kuma da dama da suka ji rauni sun fito ne domin murna shiga shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai, to amma wani dan bindiga yasa murna ta koma ciki lokacinda ya bude wuta ya karkashe mutane.
Hare haren ta’adanci ya fara zama ruwan dare gama gari a kasar Turkiya. Domin a watan jiya ma wani tagwayen harin bam da aka kai ya kashe mutane arba’in da hudu da raunata mutane dari da sittin da hudu a filin wasan kwalon kafa a birnin na Istanbul .
Kwanki goma sha daya da suka shige, wani dan sanda ya bindige jakadan kasar Rasha a birnin Ankara yana mai fadin cewa ramuwar gaiyace ga hare haren da Rasha ke kaiwa akan yan tawaye da kuma fara hula a birnin Aleppo na kasar Syria.
Tun shekara ta dubu da goma sha biyar an kashe fiye da mutane dari biyar a sakamakon hare haren ta’adanci, wadanda au yan kungiyar ISIS ko kuma yan a waren Kurdawa ke ikirarin cewa sune keda alhakin kaiwa.
Ana ci gaba da farautar dan bindigan daya kashe mutane talatin da tara da sanyin safiyar jiya Lahadi. Firayim Ministan Turkiya Binali Yildrim yace har yanzu hukumomin kasar basu da masaniyar wake da alhakin kai harin.