Kungiyoyin jama'a da shugabannin al'umma da sarakuna da 'yan kasuwa da jami'an gwamnati ne suka halarci taron.
Gwamnan jihar Bauchi shi ya fara jawabi inda ya bukaci a magance abubuwan dake kawo yaduwar 'yan ta'ada da ta'addanci.
Yace a tunkari ainihin dalilan da suka kawo faruwar masifar Boko Haram. Dalilan kuwa inji gwamnan su ne talauci da rashin ilimi da rashin walwala a arewa maso gabashin Najeriya su ne tushen 'yan ta'addan Boko Haram.
Acewar Gwamna Abubakar yakamata a kwar dasu idan ko ba haka ba nan gaba wani mahaukaci na iya fitowa ya kira kansa wani abu daban idan kuma ba'a yi hankali ba zai samu dimbin magoya baya a cikin matasa da matan da basu da aikin yi.
Wasu da aka zanta dasu sun bada shawarwari da dama. Iliyasu Aliyu sarkin gabas din Misau ya roki kwamitin ya farfado masu da masana'antunsu da suka durkushe sanadiyar rikicin Boko Haram da gidajen da aka kone. A cewarsa kowane basarake ya san wadanda lamarin ya shafa da dukiyoyin da suka salwanta.
Shi ma Kasumu Ibrahim kantoman riko na wata karamar hukuma yace duk wasu hanyoin da zasu samar ma matasa da mata aiki suka kamata a sa cikin tsarin kwamitin din tare da samun ingartacciyar wutar lantarki.
Shugaban kwamitin Yusuf Buba Yakubu yace idan har ana son a farfado da tattalin arzikin arewa maso gabas dole ne a bude hanyoyi domin bayan an yi aikin noma za'a iya fitar da kayan gona ba tare da wata matsala ba. Baicin wannan za'a horas da matasa ayyukan hannu daban daban tare da basu kayan aiki domin su samu abun yi da dogaro ga kai.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.