Shugaban kungiyar a Najeriya Farfasa Murtada Aremu Muibidin na Jami'ar Jihar Nasarawa yace a karshen taron wanda zasu kammala yau da safe zasu tattara wasu shawarwari da kuma mahimman bayanai da zasu mikawa gwamnati.
Zasu yi hakan ne domin tabbatar da gwamnati ta samu nasarar da ake bukata ta fannin yaki da cin hanci da kuma yaki da masu tayar da kayar baya.
Mataimakin shugaban kungiyar Farfasa Sani Umar Musa na Jami'ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoto yace ta hanyar kungiyoyin asiri ne a ke samun daliban dake shiga kungiyoyin ta'adanci.
Yace daga cikin kokarin da kungiyar tayi tun daga gwamnatoci daban daban tare da taimakon manyan malamai irinsu Shaikh Ahmed Lemu da sauransu, an tunkari hukuma an nuna mata cewa wajibi ne a tabbatar da ana koyas da addini a makarantu. Yace da addinin musulunci da na kirista babu wani addini da yake kira a yi ta'adanci ko kashe wasu misali. Koyas da addini zai tabbatar an sa dalibai akan tafarki mai kyau.
Dr. Abubakar Kawu Hassan shugaban kungiyar malaman Larabci na jihar Neja yace akwai wani gibi da aka bari a tsarin koyaswa dake haddasa shiga kungiyoyin ta'adanci da dalibai keyi.Yace lokacin da aka ce ba dole ba ne a koyas da addini daga azuzuwan Sakandare na gaba lokacin abubuwa suka fara tabarbarewa. Yace yaro na son addinisa yana kuma koyon karatun kumiya idan an ce masa duk mutane mazalunta ne a jefa masu bam zai yadda.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.