Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tukwicin Naira Miliyan Biyar Ga Wanda Ya Ba Da Bayanai Kan Inda Ake Hada Makamai


Manjo Janar Rogers Nicholas kwamandan Operation Lafiya Dole dake Maiduguri
Manjo Janar Rogers Nicholas kwamandan Operation Lafiya Dole dake Maiduguri

A wani sabon yunkurin kawo karshen ayyukan ta’addanci a arewa maso gabashin Najeriya kwamandan rundunar sojojin Operation Lafiya Dole ya yi tayin bada tukwuicin Naira miliyan biyar ga duk wanda ya tsegunta masu inda ake kera bama bamai.

Kwamandan rundunar soji ta Operation Lafiya Dole dake jihar Borno Manjo Janar Rogers Nicholas shi ya sanar da bada tukwuicin Naira miliyan biyar ga duk wanda zai kai su ko tsegunta musu inda ake kera bama bamai a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe.

Ya ce duk inda mutum ya san ana kera bama bamai, ya basu bayani kai tsaye zasu bada tukwuicin.

Janar Nicholas yace sun fahimci cewa inda ake kera bama baman suna cikin jama’a ne. Saboda haka sojoji zasu bada Naira miliyan biyar ga duk wanda ya kwarmata masu inda ake kera bama bamai.

Kwamandan y ace yanzu suna da ‘yan Boko Haram fiye da dari uku wadanda suka mika kansu da kansu kuma sun ‘yanto mutane fiye da miliyan daya. Kuma adadin na karuwa ne duk wayewar gari.

Akwai kuma wasu ‘yan kunar bakin wake da dama da sojojin suka katse masu hanzari da jama’a basu sani ba. An kuma kame wasun su da dama. Akwai wasu a hannun ‘yan sanda akwai wasu kuma a hannun soji.

Birgediya Abdulmalik Biu ya ce ana iya shaidawa kowane ofis din jami’an tsaro ko kuma a je fadar Shehun Borno a bada rahoto.

A saurari rahoton Haruna Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG