Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Borno: An Samar Da Garuruwan Tsira Wa 'Yan Boko Haram Dake Son Mika Kai


Kwamandan rundunar sojojin dake fafatawa da kungiyar Boko Haram Janar Rogers Nicholas
Kwamandan rundunar sojojin dake fafatawa da kungiyar Boko Haram Janar Rogers Nicholas

Rundunar sojojin Najeriya dake fafatawa da kungiyar Boko Haram a jihar Borno ta kira ‘yan ta’addan da su mika kansu da kansu domin su samu ahuwa sabili da haka ne ta kafa wuraren da zasu iya zuwa a garuwa da dama cikin jihar kuma da zara sun yi hakan za’a kula dasu ba tare da wata tsagwama ba

Rundunar sosjojin Najeriya dake fafatawa da ‘yan Boko Haram ta kira ‘yan kungiyar da su mika kansu da kansu domin a yi masu ahuwa maimakon su yi asarar rayukansu.

A wata fira da ya yi da Muryar Amurka kwamandan rundunar sojojin dake fafatawa da kungiyar Boko Haram din, Manjo Janar Rogers Nicholas ya bayyana shirin da suka yi domin karbar wadanda, watakila, zasu tuba su fito da gaske daga kungiyar ta’addancin.

A cewar kwamandan sun bude wasu wuraren da ‘yan ta’addan ka iya zuwa su mika kansu ba tare da wata matsala ko tsangwama ba. Injishi sun basu zabi ne saboda sun ji akwai wasunsu da suke son su fito daga kungiyar.

Dangane da yadda zasu mika kansu, Janar Nicholas ya ce mutum na iya daga hannunsa ko ya fitar da farin kyale a matsayin alamar mika kai. Duk wanda ya yi hakan babu wanda zai taba shi. Ya ce idan sun fito da gaske zasu ciyar dasu, su basu sutura tare da kula da lafiyarsu. Zasu kuma mika kayan yakinsu.

Akan tabbacin da rundunar zata ba wadanda suka fito din, Janar Nicholas ya ce wadanda suka fito da suka karbesu suna nan ba’a yi masu komi ba. Su ne shaida kuma ya kara da kiran ‘yan jarida su je su gani da idanunsu, domin gani ya kori ji.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG