Gwamnatin jihar Borno ta horas da wasu matasa 2900 da zasu dinga samar da tsaro a dukkan kananan hukumomin jihar.
Gwamnan jihar Kashim Shettima shi ya kaddamar da shirin. Yace matasan zasu dinga samar da tsaro ne, kuma zasu rika yin aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro.
Matasan da aka horas zasu dinga sa ido ne akan makwaptan su. An umurci matasan cewa da zara sun ga wanda basu yadda dashi ba ko kuma wani abu su sanar da jami’an tsaro ba tare da bata wani lokaci ba.
Gwamnan ya kuma yabawa matasan akan irin kokarin da suka yi wajen taimakawa. Matasan sun yi alkawarin aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata.
Kwamishanan shari’a na jihar Alhaji Kaka Shehu Lawan ya kara yiwa matasan bayanin irin ayyukan da zasu yi da suka hada da bada taimakon gaggawa ga marasa lafiya
Saurari cikakken rahoton Haruna Dauda
Facebook Forum