Rundunar da ke yaki da ta’addancin Boko Haram a jihar Borno, Operation Lafiya Dole ta ceto mutane sama da 1,000 daga hannun kungiyar.
Wata sanarawa dauke da sa hannun Kakakin rundunar sojin Najeriya, Brig. Gen. Texas Chukwu a yau Litinin a ta ce rundunar tare da rundunar hadin gwiwar kasashe ta MNJTF, sun ceto mutane daga kauyuka hudu da suka hada da Malamkari, Amchaka, da Walasa da Gora da ke karamar hukumar Bama a Jihar Borno.
Sanarwar ta bayyana cewa, aksarin wadanda aka ceto mata ne da yara kanana da wasu matasa da aka tilastawa zama mayakan Boko Haram. A yanzu suna asibitin soji domin a duba lafiyarsu.
Facebook Forum