Yayin da ake jiran bayyana da aka ce Shugaba Muhammadu Buhari zai yi a gaban Majalisar Tarayyar Najeriya gobe Alhamis, tuni aka fara jayayya kan tsarin bayyanar da kuma salon ba’asin da zai bayar game da tabarbarewar tsaro a Najeriya.
A wani mataki na warware zare da abawa a harkar tsaro da ke addabar Najeriya ne Majalisar Wakilai ta gayyaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya bayyana a gabanta domin amsa tambayoyi, kuma Shugaban Kasa ya amsa kira. To saidai wasu ‘yan Majalisar na ganin ba za a wanye lafiya ba, saboda ‘yan Majalisar sun fusata, musamman ma ‘yan adawa da ke kiran da a tsige Shugaban kasar.
Wannan gayyata da Majalisar Wakilai ta yi wa Shugaba Mohammadu Buhari ita ce irin ta na farko tunda ya hau karagar mulki a shekara 2015.
Gayyatar ta biyo bayan kudurin doka ne da wasu mambobin Majalisar daga jihar Barno suka gabatar akan kisar gillar da 'yan Boko Haram suka yi ma wasu manoma akalla 43 a jihar..
To saidai duk da cewa Shugaba Buhari ya amsa gayyatar kuma har an sa rana - cewa gobe Alhamis ne bayyana, amma al'amarin yana neman daukar sabon salo domin an ce ba Majalisar Wakilai kadai zai je ba, za a yi zaman hadin gwiwa ne da Majalisar Dattawa, wani abu da Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa ya ce akwai abin dubawa, domin ya kamata a aiko da wasika zauren Majalisar dattawa akan hakan, a kuma karanta ta kowa ya amince tukuna, in ba haka ba zaman, to hadin gwiwa zai yi wuya.
A lokacin da yake nashi nazarin, Shugaban Kwamitin Kula da Harkokin Sojin Sama a Majalisar Wakilai, Shehu Mohammed Koko ya ce ba daidai ba ne Majalisar Wakilai ta yi kuduri na gayyatar Shugaban kasa, amma kuma a hada su da Majalisar Dattawa. Ya ce shi baya goyon bayan gayyatar, domin Shugaban Kasar ba zai fadi wani abu daban da wanda shugabanin hukumomin tsaro ke fada kullum ba. Koko yana ganin abinda ya dace kawai shi ne a zauna da shi cikin sirri domin haka harkar tsaro ta gada.
A wani abu mai kamar mayar da martani, Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Yahaya Abdullahi Abubakar, ya ce kafin a yi zaman hadin gwiwa sai Majalisun biyu sun amince tukuna, kuma a irin wanan yanayi da wasu ke nuna fushi da abubuwan da ke faruwa a kasa, yana ganin barin yin taron gaba daya zai fi, inda ya bada shawarar Shugaba Muhammadu Buhari yayi wa kasa jawabi ta kafafen yada labarai.
Tun dai a daren jiya Talata ne Shugaba Muhammadu Buhari yake ta tarurruka da Gwamnoni akan batun tsaron kasa. Abin jira a gani shi ne ko sakamakon tarurrukan zai sa Shugaba Muhammadu Buhari ya canja ra'ayinsa a game da zuwa Majalisar, lokaci ne kadai zai baiyana haka.
Ga Madina Dauda da cikakken rahoton: