Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Musulmi Ya Bukaci a Yawaita Addu’o’i Don Samun Zaman Lafiya a Najeriya


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar.
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar.

Shugaban Majalisar Koli kan lamurran addinin Musulunci mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar, ya bukaci musulmi da su yawaita zama masallatai suna addu'a domin samun waraka daga matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya yi wannan kira ne a wurin babban taron manoma da sarrafa Dibino a Najeriya da aka yi a Sokoto. Ya ce yin hakan zai iya yin tasiri sosai wajen samun mafita daga matsalolin rashin tsaro da ke haddabar kasar nan.

“Ina kira ga dukkannin mu musamman musulmi na wannan kasa, da mu rika tsayawa a masallatai idan muka je sallah sau biyar a rana, da kuma sallar Juma'a koma a duk inda muka samu kanmu, a ci gaba da yin addu'a ga wannan kasa domin neman gafara daga Allah da jin kai mu samu fita daga wannan kangi na kaluballale da muke fuskanta".

Dangane kisan manoman Shinkafa da aka yi a jihar Borno, Mai alfarma sarkin musulmi ya nuna bacin rai.

Ya ce “Babban abin muni ne abin da ya faru a Borno ‘yan kwanakin da suka wuce, yana daya daga cikin kisa mafi muni da aka yi a kasar nan, amma dole mu koma ga Allah a koda yaushe domin shine ke yin yadda ya so a lokacin da yaso, ba muna kalubalantar hukuncin Ubangiji ba ne, sai dai muna kara gode masa akan, farkar da mu shugabannin ga hakkin da ya rataya akan mu domin zai tambaye mu akan nauyin da ya dora mana".

Yin amfani da shawarwarin shugabannin addinai da na al'umma kan iya zama sila ta samarwa da mabiya ga abin da suke nema, musamman yanzu da jama'a ke ta kokawa a kan matsalar rashin tsaro a Najeriya.

Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG