Alhaji Bashir Yusuf Ibrahim shugaban sabuwar jam'iyyar PDM na kasa ya ce kafin Najeriya ta smu cigaba dole al'ummar kasar ta yi watsi da ban-bance ban-bancen addini da na kabilacin wadanda suke so su yiwa kasar katutu su nakasar da ita. Ya yi jawabi ne a taron jam'iyyar na shiyar arewa maso yamma da aka yi a birnin Kaduna. Ya ce duk wani alkawarin 'yan siyasa da can cewa za'a gina makarantu da asibitoci da hanyoyi duk karerayayi ne. Ya ce azzaluman shugabanni da suka mamaye shugabancin kasar suna raba kawunan mutane da yin anfani da addini da kabilanci da bangaranci domin cigaba da zaluntar mutane. Kasar na cikin wani yanayi inda duk wannda ya zo shugabanci yana kokarin ya yagi nashi kana ya yi gaba. Babu kishin kasa ko tandawa talakawa. Akwai rashin adalci. Akwai rashin gaskiya. Ya ce shi ne dalilin da ya sa PDM ta fito ta gyara lamarin domin kasar ta cigaba.
Ganin irin talaucin da ya addabi 'yan Najeriya ya sa PDM ta yunkura ta yaki wannan mugun bala'i. Yanzu kusan 'yan Najeriya kashi tamanin da biyu ke fama da talauci. Idan Allah ya baiwa PDM mulki zata rage talauci. Kawar da shi gaba daya ba zai yiwu ba yanzu. Alhaji Bashir Yusuf Ibrahim ya ce wajen shekara goma ke nan suna gwagwarmaya a cikin jam'iyyar PDP amma abun ya gagara sabili da haka suka fita suka nemi yiwa PDM ragista.
Isa Lawal Ikara nada rahoto.