Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Umarci A Takaita Shagulgula A Bikin ‘Yancin Kan Najeriya Na 64


Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar Ma'aikata ta Duniya
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar Ma'aikata ta Duniya

Sanata George Akume yace gwamnatin Shugaba Tinubu na sane kuma ta na tausayawa ‘yan Najeriya game da halin matsin tattalin arzikin da suke ciki, don haka aka takaita shagulgulan da za a gudanar a bikin.

A karo na 2 a jere, gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar takaita shagulgulan bikin samun ‘yancin kan Najeriya da zai gudana a ranar 1 ga watan Oktoba mai kamawa saboda halin matsin da kasar ke ciki.

A hirarsa da manema labarai yayin baje kolin shagulgulan da aka tsara gudanarwa a ranar bikin samun ‘yancin kan, sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume yace gwamnatin Shugaba Tinubu na sane kuma ta na tausayawa ‘yan Najeriya game da halin matsin tattalin arzikin da suke ciki, don haka aka takaita shagulgulan da za a gudanar a bikin.

An takaita shagulgula a bikin samun ‘yancin kan Najeriya na 63 a bara inda Sanata Akume, yace ba za a gayyaci shugabannin kasashen ketare ba, saboda halin matsin tattalin arzikin da kasa ke ciki.

A yayin ganawar ta jiya Alhamis, Akume yace an yanke shawarar ne a bisa la’akari da halin da kasa ke ciki, don haka Shugaba Tinubu ya amince a takaita shagulgula a bikin ‘yancin kan Najeriya na 64.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG