A bana dai ba a gudanar da bikin 'yancin kan Najeriyar ba a ofisoshin jakadun kasar da ke sassan Turai da dama kamar yadda aka saba gudanarwa a duk shekara, bikin da ke hada kan ‘yan kasar mazauna Turai tare da nuna wa duniya al’adunta.
Babu dai takaimaimen bayani ko dalilin kan soke bikin na bana a Jamus da Belgium da kuma Ingila a binciken da Muryar Amurka tayi.
A can Najeriya dai, bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan kasar da dama ke kuka da matsin tattalin arziki da hauhawar farashi sakamakon janye tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tayi a ranar ta farko ta hawansa mulki a watan Mayun da ya gabata.
Shekaru 63 da samun ‘yancinta daga Birtaniya har yanzu wasu ‘yan Najeriya na ganin Burtaniyan na ci gaba da cin moriyar kasar ta la’akari da yadda ta zama kasar da ake da mafi yawan al’ummarta a Turai kamar yadda rahotanni ke nunawa a baya-bayan an yi ta dambarwa kan yadda akasarin kwararrun likitocin Najeriyar ke tserewa zuwa Burtaniya duk da karancinsu a kasar.
Dakta Paul Oynekachi daya daga cikin jagoririn kungiyar ‘yan Najeriya mazauna Jamus ya ce, akwai bukatar a yi wa tufkar hanci,
''Baya ga cewa kasar ce tayi wa Najeriya mulkin mallaka, tana da bukatar wadannan likitocin sosai, shi yasa take jan hankalinsu ta hanyar basu kulawa da tsaro saboda a Najeriya babu tsaro likita ba shi da tabbas kan tsaron ransa da zarar yasa kafa ya bar gida rayuwarsa na cikin hadari’'
Duk da wadannan matsalolin akwai ‘yan Najeriya mazauna Turan da ke da yakinin cewa al'amura za su inganta ganin tarin basirar da ke tattare da ‘yan kasar.
Ruth Keeng na daga cikin masu wannan fata. Ta ce "Najeriya kasa ce mai abubuwa na ban sha’awa kamą daga basirar kwallon kafa da mawaka da kwararrun likitoci ga marubuta da sauransu, muna da arziki da masu ilimi da fasahar da ke jan hankalin duniya, ni ina alfahari da kasata Najeriya ina kumą mata fatan alkhairi Allah ya daukaka Najeriya ina yi wa al’ummarta barka da bikin cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai’’
Najeriya ce dai kasa mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika kuma duk da arzikin da Allah ya huwace mata jama’arta da dama na fama da talauci, matsalar da masana ke dangantawa da manyan kalubale na cin hanci da rashawa a kasar da ta çıka shekaru 63 da samun ‘yancin kai daga turawan Birtaniya ke fuskanta.
Saurari rahoton Ramatu Garba Baba:
Dandalin Mu Tattauna