Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutane 11 A Neja

Wasu mazauna Maiduguri suna yin kaura bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye unguwanninsu (Hoto: Facebook/NEMA)
Wasu mazauna Maiduguri suna yin kaura bayan da ambaliyar ruwa ta mamaye unguwanninsu (Hoto: Facebook/NEMA)

Babban darktan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, Abdullahi Baba-Arah, ya bayyana tsananin lamarin a sanarwar da ya fitar.

Iftila’i ya afkawa jihar Neja sakamakon ambaliyar ruwan da ta hallaka mutane 11, tare da daidaita garuruwa da haddasa mummunar barna a 19 daga cikin kananan hukumomin jihar 25.

Ambaliyar ta malale gonaki 118, 692, inda ta jefa dimbin mazauna yankin cikin halin rashin tabbas sakamakon mummunar illar da ta yiwa sana’o’insu.

Baya ga lalata gonaki, ambaliyar ta shafi makarantu 246, inda ta kawo tsaiko a harkar koyo da koyarwa a garuruwa 529. Barnar ta kuma shafi garuruwa 34 a jumlance, inda ta jefa mutane 41, 192 cikin matsanancin halin neman agaji da dauki.

Kananan hukumomin da ambaliyar tafi kamari sun hada da Mokwa da Katcha da Lavun da Lapai da Agaie da Shiroro da Munya da Gbako da Kontogora da Bosso da Edati da Agwara da Bida da Magama da Mashegu da Borgu da Gurara da Suleja da kuma Rijau.

Babban darktan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja, Abdullahi Baba-Arah, ya bayyana tsananin lamarin a sanarwar da ya fitar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG