Hukumar kula da kogunan Najeriya (NHSA) ta jaddada bukatar mazauna kusa da gabar kogunan neja da benuwe dasu gaggauta kauracewa zuwa yankunan da basu da hatsari domin tsira da rayuka da dukiyoyinsu.
A sanarwar daya fitar a yau Juma’a, babban daraktan NHSA, Umar Muhammad ya sake nanata cewar tumbatsar da kogunan 2 suka ta kai mizanin gargadi.
Ya kuma jaddada bukatar ‘yan Najeriya su kiyaye gargadin hukumar, ta hanyar yin abinda ya dace-na yashe magudanan ruwa da kwatocinsu domin baiwa ruwan sama damar gudanawa.
Ya ci gaba da cewa tsawaitar da damina ta yi a fadin kasar nan ce ta haddasa munanan ambaliyar ruwan da ake gani.
Dandalin Mu Tattauna