Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bude sabon babin caccakar zaman sauraren shaidu a yunkurin tsige shi da za’a soma a wannan makon, inda ya bayyana shi da “abin kunya da tozartawa”, ya kuma yi korafin cewa ‘yan jam’iyyar Democrats, suna toshe kafa ga wasu shaidun da ‘yan Republican suke son tambaya.
Trump ya ce gurbataccen dan siyasa Adam Schiff, shugaban kwamitin leken asiri na majalisar wakilai da ke jagorantar yunkurin tsige shi, da kuma kakakin majalisar Nancy Pelosi, suna son jami’an White House su bayar da shaidar bi-ta-da-kulli.
A karkashin dokokin yunkurin na tsige shugaban kasa da majalisar mai rinjayen ‘yan Democarts ta shata, za’a baiwa Trump damar samun lauya mai wakiltar shi, idan kwamitin majalisar mai kula da sha’anin Shari’a ya aminta da shaidun tsige shi a makwanni masu zuwa, da kuma idan daukacin majalisar ta tsige shi, a zaman bin bahasin tsigewar a majalisar dattawa, da ke da rinjayen ‘yan Republican.
To sai dai dokokin ba su baiwa Trump damar a wakilce shi ba a zaman sauraren shaidu na kwamitin leken asiri na majalisar wakilan da za’a soma ranar Laraba.
Jami’an ma’aikatar harkokin wajen Amurka biyu, William Taylor da George Kent, sun shirya tsaf, domin ba da shaidar cewa Trump ya tilastawa Shugaban kasar Ukrain, Volodymyr Zelenskiy gudanar da bincike da zai yi amfani shi a siyasance, a daidai sa’adda ya rike tallafin sojin Amurka dalarmiliyan 391, da Kyiv ta ke matukar bukata domin tallafa mata a yaki da ‘yan awaren da ke da goyon bayan Rasha a gabashin kasar.
Facebook Forum