Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakada Sondland Ya Yi Gyara A Ba'asin Da Ya Bayar A Binciken Trump


Wani jigo cikin jami’an diplomasiyyar Amurka, ya fada wa kwamitocin da ke binciken yiwuwar tsige Shugaba Donald Trump cewa, ya gano cewa an ki sakar tallafin kusan dala miliyan dari-hudu na kayayyakin soji da Amurka ta ware wa Ukraine, har sai hukumomin Kyiv sun fito bainar jama’a sun ce za su kaddamar da bincike, domin taimakawa siyasar Shugaba Trump.

A wani bitar bahasin da ya bayar a jiya Talata, jakadan Amurka a kungiyar Tarayyar Turai, Gordon Sondland ya fadawa masu binciken na majalisar wakilan Amurka cewa, ya gargadi wani na hannun daman shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy a wani zama da suka yi a ranar daya ga watan Satumba a birnin Warsaw, da cewa, ba za su samu tallafi daga Amurka ba, har sai Ukraine ta fito fili ta sanar da shirin yaki da cin hanci da rashawa, da aka kwashe makonni da dama ana tattaunawa akai.

Sondland, wanda na daya daga cikin na gaba-gaba da suka ba Shugaba Trump gudunmuwa a bikin murnar lashe zabe a shekarar 2017, na nuni ne da bukatar da Trump ya gabatar a karshen watan Yuli, ga Shugaba Zelenskiy, yayin wata tattaunawa da suka yi ta wayar tarho, inda ya nemi a binciki daya daga cikin manyan abokanan hamayyarsa na siyasa, tsohon mataimakin shugaban Amurka Joe Biden da dansa Hunter, wanda ya yi aiki da wani kamfanin gas a Ukraine, da kuma duk wata sheda da za ta nuna cewa Ukraine ta yi katsalandan a zaben Amurka na 2016, wanda ya ba shi damar darewa karagar mulki.

Sai dai ‘yan Republican sun tsaya tsayin daka suna ci gaba da nuna goyon bayan ga Trump a wannan bincike da ake yi akansa, - Kevin McCarthy shi ne shugaban ‘yan Republican a majalisar wakilan Amurka, ya ce, “’yan Democrat na kokarin su tsige shugaban ne, saboda suna fargabar ba za su iya ka da shi a zabe ba.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG