Za a fara gudanar da binciken da ke duba yiwuwar tsige shugaban Amurka Donald Trump a baina jama’a a mako mai zuwa, binciken da ke kokarin gano gaskiyar zargin cewa Trump ya yi yunkurin tursasawa Ukraine ta binciki daya daga cikin wadanda suke so su fafata da shi a zaben shugaban kasa na 2020 a bangaren ‘yan Democrat, inji shugaban kwamitin da ke kula da tattara bayanan sirri a majalisar wakilan Amurka, Adam Schiff.
Schiff ya ce, “a ranar Laraba, za mu fara da sauraren shaidar jakada Taylor da jakada Kent, sannan a ranar Juma’a mu saurari Jakada Yovanovitch.”
A jiya Laraba Schiff ya bayyana hakan, bayan da aka kwashe makonni ana sauraren shaidu cikin sirri, inda ya ce, Amurkawa za su samu damar yin alkalanci da kansu kan wannan bincike.
Bill Taylor, babban jami’in diplomasiyyar Amurka ne a Ukraine, shi kuwa George Kent, shi ne mataimakin Karamin Sakataren Harkokin wajen Amurka, wadanda da su binciken na bainar jama’a zai yi karin kumallo a ranar Laraba.
Facebook Forum