Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Daukaka Kara Kan Hukuncin Hana Shi Shiga Zaben Jihar Maine


Tsohon shugaban kasar Amurka DOnald Trump
Tsohon shugaban kasar Amurka DOnald Trump

A jiya Talata tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya daukaka kara kan hukuncin da sakatariyar harkokin wajen jihar Maine ta jam’iyyar Democrat ta yanke, na haramta masa takara.

WASHINGTON, D. C. - Haka ya faru ne bisa rawar da ya taka a harin da aka kai wa Majalisar dokokin Amurka a ranar 6 ga Janairun shekarar 2021.

Ana sa ran zai kuma bukaci kotun kolin Amurka da ta yanke hukunci kan cancantarsa na komawa takarar Shugaban kasa a wata shari'a mai kama da wannan a jihar Colorado.

Dan takarar na jam’iyyar Republican ya daukaka kara kan hukuncin jihar Maine da Shenna Bellows ta gabatar, wacce ta zama sakatariyar harkokin wajen jiha ta farko a tarihi da haramta wa wani tsayawa takarar shugaban kasa, a karkashin sashe na 3 na doka ta 14 da aka yi wa kwaskwarima, wacce ba kasafai ake amfani da ita ba.

Tanadin dokar ya haramta wa wadanda suka “yi tawaye” rike mukami. An daukaka karar ne zuwa Babbar Kotun Maine.

Ana kuma sa ran Trump zai daukaka kara kan irin wannan hukuncin da kotun kolin Colorado ta yanke kai tsaye zuwa kotun kolin Amurka.

Kotun kolin kasar ba ta taba yanke hukunci kan sashe na 3 ba, kuma hukuncin da kotun Colorado ta yanke wa Trump, shi ne karo na farko a tarihi da aka yi amfani da dokar don hana wani dan takarar shugaban kasa shiga zabe.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG