Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Samun Karin Mutanen Da COVID-19 Ta Kama a Amurka


Wata jami'ar lafiya a Amurka
Wata jami'ar lafiya a Amurka

Ana samun ra'ayoyi mabanbanta a tsakanin gwamnonin jihohin Amurka kan yadda za a bullowa cutar coronavirus.

Adadin sabbin wadanda suke kamuwa da coronavirus a Amurka sai kara hauhawa yake, yayin da gwamnonin jihohi ke ba da sakonnin masu karo da juna kan yadda za a magance wannan annoba.

Ana samu wadanda suke kamuwa a kullum sama da dubu 60,000, abin da ya saka daya daga cikin manyan shagunan sayar da kayayyakin na Walmart, ya bukaci dole kwastomominsa su rika saka kyalen rufe baki da hanci a rassansa dubu 5,000.

Gwamna Kay Ivey na jihar Albama da ke kudancin Amurka ya umarci duk mazaunan jihar da su fara saka takunkumin rufe fuska daga jiya Alhamis, yayin da jihar ta ba da rahoton samun kusan sabbin mutum 50 da suka mutu a ranar Laraba.

Gwamnan Montana, Steve Bullock da ke yammacin Amurka ya ce dole ne a saka takunkumin rufe fuska a dukkan wuraren taruwar jama’a a kananan hukumomi inda mutum 4 ko sama da haka aka gwada su suna dauke da COVID-19.

Amma a jihar Georgia da ke kudancin Amurka, inda aka samu kusan mutum dubu 3,900 a matsayin sabbin wadanda suka kamu, wanda shi ne adadi mafi yawa tun lokacin da annobar ta fara.

Gwamnan jihar dan jam’iyyar Republican, Brian Kemp, ya fitar da wata sabuwar doka da ta hana garuruwa tilasta saka takunkumi, duk da cewa yana ba mutane kwarin gwiwar su rika saka takunkumin

Ya kuma fadada dokar yin nesa-nesa da juna a fadin jihar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG