Cikin kwanaki biyu a jere, a ranar 18 ga watan Yuli hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 na tarihi a fadin duniya, yayin da aka samu mutum 260,000 da suka kamu da cutar cikin sa’o’i 24. A ranar Juma’a 17 ga watan Yuli kwana daya kafin ranar, an samu mutum 238,000 da suka kamu da cutar.
Zuwa yammacin ranar Asabar, hukumar ta tattara adadin mutum sama da 593,000 da suka mutu sanadiyyar COVID-19, cutar da coronavirus ke janyowa. Wannan karin ya zarta na mutum 7,300, adadi mafi yawa da aka samu a rana guda tun cikin tsakiyar watan Mayu. Adadin mace-macen da ake samu ya na kai kusan 4,800 a duk rana a watan Yuli.
Kasashen da aka samu karin mai yawa sun hada da Amurka, inda aka samu kusan mutum 72,000, sai Brazil da ta samu kusan 45,000, India kuma ta samu karin kusan mutum 35,000, daga nan sai Afrika ta kudu inda aka samu kusan mutum 14,000.
A Brazil, kasar da cutar ta fi shafa a nahiyar Amurka ta kudu, Shugaba Jair Bolsonaro ya fada a ranar Asabar cewa matakan dakile yaduwar cutar da aka dauka na shafar tattalin arzikin kasar sosai.
Facebook Forum