Rahotannin baya-bayan nan dake fitowa daga Maiduguri sun bayyana cewar mummunar ambaliyar ruwa ta raba birnin da sauran sassan jihar.
An ruwaito labarai masu ban tausayi na mutuwar dabbobi da rufe wuraren kasuwanci da makarantu sakamakon ambaliyar da ta malale ilahirin birnin.
Bincike ya gano cewa mazauna birnin na zama cikin zulumi sakamakon mamaye yankin da kadoji da macizai da sauran miyagun dabbobi suka yi, musamman a yankunan gidan waya (Post Office) da kasuwar Monday dake makwabtaka da gidan adana namun daji na Shehu Kyarimi.
An kuma kara gano cewa baya ga fadar Shehun Borno da wani bangare na jami’ar Maiduguri da asibitin koyarwar ta da unguwannin Gwange da Mormoro da rukunin gidaje 500 na Abbagana da shahararriyar kasuwar nan ta Monday da babban titin Legas da Cibiyar ‘Yan Jaridu hatta gidan gwamnatin jihar ma ruwa ya mamaye, al’amarin daya raba miliyoyin mutane da gidajensu tare da lalata dukiya ta biliyoyin nairori.
Dandalin Mu Tattauna