An tabbatar da mutuwar akalla mutane 20 sakamakon rugujewar gidaje sanadiyar mamakon ruwan sama, makonni 2 da suka gabata a garin Gashua, shelkwatar karamar hukumar Bade ta jihar Yobe.
Shugaban karamar hukumar, Babagana Ibrahim ya shaidawa wakilin tashar talabijin ta Channels cewa, galibin mazauna garin na samun mafaka ne a wasu sansanoni 3 da aka ware.
A cewarsa, gwamnati na samar da muhimman bukatun ‘yan gudun hijirar da suka hada da kayan abinci da magunguna da kayan tsaftace muhalli da ruwan sha da abinci mai tsafta domin magance barkewar cututtuka.
Babagana Ibrahim ya kuma nemi karin tallafi daga gwamnatin tarayya da hukumomin bada agaji.
An ruwaito shi yana cewa, “adadin wadanda suka rasa muhallansu ya karu zuwa kusan dubu 3, muna bukatar gwamnatin tarayya da hukumomin bada agaji su tallafawa jihohi da kananan hukumomin da ibtila’in ambaliyar ruwa ta afkawa ta hanyar sama musu da kayan agaji.”
Ana samun ruwan sama a ‘yan kwanakin nan kuma gidaje da dama musamman na kasa ke rushewa. Da safiyar yau kawai, an tabbatar da mutuwar mutane 4 a Gashua.”
Dandalin Mu Tattauna