Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA a Najeriya ta sanar da irin matakan da mutane za su iya dauka don kare aukuwar ko fada wa kangin ambaliyar ruwa a yankunan da aka yi hasashen za su iya fuskantar wannan ibtila’i.
A karshen makon da ya gabata NEMA ta yi hasashen yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin da ke tsakiya da kudancin Najeriya.
Cikin watan sanawar da ta wallafa a shafinta na Facebook, hukumar ta NEMA ta ce cikin makonnin masu zuwa jihohin Benue, Kogi, Anambra, Delta, Imo, Rivers da Bayelsa za su fuskancin mamakon ruwan sama.
Hakan ya sa hukumar ta yi kira ga hukumomin jihohin da al’umominsu da su zauna cikin shiri tare da ba su shawara kan matakan da za su iya dauka kafin aukuwar ambaliyar ruwan.
Shawarwari da hukumar ta NEMA ta bayar sun hada da:
Gyara Magudanan Ruwa: Hukumar ta NEMA ta yi kira da a tabbatar dukkan magudanan ruwa da suka toshe an bude su domin ruwa ya samu gudana ba tare da wata tangarda ba.
Gina Shingaye: NEMA ta kara da cewa wata hanya da ke taimaka wa wajen kare ambaliyar ruwa ita ce gina shingaye ta hanyar jera buhunhunan yashi a inda ake tunanin ruwa zai iya mamaye wa.
Kaurace wa Wuraren Da Ke Da Hadari: A cewar hukumar ta NEMA, yana da kyau a kwashe mutanen da ke zaunen a yankunan da ke da hadarin fuskantar ambaliyar ruwa a mayar da su yankunan ko tuddan da ba su da hadari.
“Muna kira ga dukkan mazauna yankunan da su bi shawarwarinmu su dauki matakan kandagarki domin kare rayuka da dukiyoyi. Kasance wa cikin shiri zai taimaka matuka wajen rage mummunan tasirin da ambaliyar ruwa ke haifarwa.” In ji shugabar hukumar NEMA ta kasa, Zubaida Umar.
Dandalin Mu Tattauna